DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shehu Sani ya fadi dalilin barinsa PDP ya koma APC

-

Tsohon Sanatan jihar Kaduna Shehu Sani ya ce Gwamnan Kaduna Uba Sani ne ya yi sanadiya komawar sa jam’iyyar APC, bayan wani zaman sulhu a jihar.
Dan gwagwarmayar ya tabbatar da cewa yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC a jihar Kaduna kuma ya bayar da gudunmawa wajen dora jam’iyyar a kan turba.
Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels, Shehu Sani ya kuma bayyana cewa takun-saka da ta shiga tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ita ce ta yi sanadin fitar sa jam’iyyar a baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

FIFA ta sanya $60 a matsayin kudin tikitin kallon kofin duniya na 2026

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ƙaddamar da sabon rukuni na tikiti a dalar Amurka 60 ga kowane ɗayan wasannin 104 na Gasar Kofin...

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a Ingila

Ƙungiyar British Medical Association (BMA) ta tabbatar da ci gaba da gudanar da yajin aiki, bayan kashi 83 cikin ɗari na mambobinta sun amince da...

Mafi Shahara