DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tinubu ya haramtawa wasu mukarraban gwamnati zuwa Amurka

-

Google search engine
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya haramtawa jami’an gwamnati wadanda basu da alaka ta kai tsaye da taron majalisar dinkin duniya zuwa wajen taron.
Shugaba Tinubu ya bada umarnin a dakatar da Shirin karbar Visar da ake yiwa jami’an gwamnatin wadanda babu wata gudumowa da zasu bayar idan sun halarci taron.
Kakakin shugaban Ajuri Ngelale ta cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce wannan na cikin kokarin da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi na rage kashe kudade baji ba gani da gwamnati ke yi.
Sanarwar ta kuma kara da cewa an dorawa ministoci da manyan shugabannin hukumomin gwamnati da su sanya idanu wajen ganin ma’aikatan su basu tafi Amurka wajen taron ba matukar dai basu da abin yi a wajen.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Za mu yi sabuwar jam’iyya ne saboda gwamnatin APC ta gurbata jam’iyyun adawa – Nasir El-Rufa’i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa jiga-jigan ‘yan adawa na son fitowa da sabuwar jam’iyyar ne gabanin zaben 2027, saboda kutsen da...

An kama mutane 22 kan harin da aka kai wa ’yan Kaduna a jihar Filato – Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa an kama mutane 22 da ake zargi da hannu a kisan wasu ‘yan asalin jihar su...

Mafi Shahara