DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tinubu ya dakatar da kaddamar da sabbin jami’o’i 37 da Buhari ya amince da su – Minista

-

Gwamnatin Tarayya ta ce za a samu jinkiri kafin sabbin jami’o’i 37 da gwamnatin da ta shude ta amince da su su fara aiki.

Google search engine

Ministan Ilimi Tahir Mamman ya bayyana haka jim kadan bayan ya yi wata ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Laraba a Abuja.

Ministan ya ce hakan ya kasance ne bisa la’akari da bukatar za a  samar wa da jami’oin da ingantattun shirye-shirye domin bayar da ingantacen ilimi.

Tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ne dai ya amince da sabbin jami’oin guda 37 kwanaki kadan kafin ya mika mulki ga gwamnatin shugaba Tinubu.

Rahoto: Ahmad Rabe Yanduna/Umar Ibrahim

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara