DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Matakin gwamnati kan digiri ‘dan Kwatano’ ya shafi daliban Nijeriya 15,000

-

Google search engine

Ƙungiyar ɗaliban Najeriya (NANS) a jamhuriyar Benin ta bayyana cewa sama da dalibai 15,000 ne suka shiga halin kaka-ni-kayi, sakamakon haramta wasu jami’o’i da gwamnatin Nijeriya ta yi a kasar.

Shugaban ƙungiyar a Jamhuriyar Benin, Ugochukwu Favor, ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawa da ya yi da gidan talabijin na Channels.

A yayin tattaunawa Favor ya yi kira da a sassauta wannan mataki musamman a kasashe Benin da Togo.

Hakan dai na zuwa ne bayan da wani ɗan jarida mai binciken kwakwaf ya fallasa yadda ake samun takardar shaidar kammala makarantun a kasashen.

Shugaban kungiyar daliban ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi bincike mai zurfi don gano wadanda ke da hannu a badakalar kuma a hukunta su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Kaduna ta yi watsi da ikiranin da El-Rufai ya yi kan ayyukan da Tinubu ya kaddamar cewa shi ne ya fara su

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da ikirarin da wani tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai ya yi na cewa dukkanin ayyukan da shugaban kasa Bola...

‘Yan majalisar wakilai sun nemi gwamnatin tarayya ta gina sansanin sojoji a Yelwata da ke jihar Benue

Majalisar Wakilai ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kafa sansanin sojojin Nijeriya a garin Yelwata dake kan iyaka a karamar hukumar Guma...

Mafi Shahara