DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu ya taya murna ga sabon shugaban kasar Chad

-

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya taya zababben shugaban kasar Chad Mahamat Idris Deby murna bayan nasarar lashe zaben shugaban kasa da ya yi.
Shugaban na Nijeriya ya hakikance cewa yadda aka gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe a kasar, ya nuna karara yadda al’ummar kasar Chad ke son dimokradiyya ta dore yadda ya kamata.
A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban kasa Mr Ajuri Ngelale, ta ce Nijeriya za ta yi aiki kafada da kafada da kasar Chad ganin yadda kasashen biyu suke mayar da hankali wajen inganta tsaro da zaman lafiya.
Shugaban kasar ya yi kiran da a cigaba da hadin kai a tsakanin kasashen biyu, sannan ya yi addu’a ga sabon shugaban kasar da ya sauke nauyin al’umma da ke kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara