DCL Hausa Radio
Kaitsaye

APC na zawarcin Gwamnan jihar Plateau

-

Gamayyar kungiyoyin jam’iyyar APC na Arewa ta tsakiyar Nijeriya na zawarcin Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwang da ya ajiye jam’iyyarsa ta PDP ya koma jam’iyyar APC.
Shugaban gamayyar kungiyoyin Saleh Mandung Abdullahi a cikin wata sanarwa da ya aike wa DCL Hausa, ya ce kiran ya zamo wajibi domim burinsu shi ne jam’iyyar APC ta kara bunkasa, amonta ya kai ko’ina.
A cikin wasikar mai taken “gayyatar Gwamna Caleb Mutfwang zuwa jam’iyyar APC” ta ce a ‘yan kwanakin nan sun gana da masu ruwa da tsaki da jigogin jam’iyyar APC na arewa ta tsakiyar Nijeriya, inda suka bukaci da a sada gwamnan da takardar gayyata, ta ya koma APC.
Hon Saleh Zazzaga ya ce tuni sun fara isar da sakon ga Gwamnan ta hanyar kafafen sadarwa, yanzu kuma sun mika masa wasika a hukumance.
Kungiyar ta ce kiran nasu ga Gwamnan jihar zai ba APC damar sake karbar jihar Plateau bayan da ta rasa ta a zaben shekarar 2023.
Wasikar ta yi nuni da cewa Gwamnan jihar Plateau Caleb Mutfwangne tilo daga yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya da ba dan jam’iyyar APC ba, don haka ne suke bukatarsa da ya saje da sauran ‘yan’uwansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Yan kasuwar mai sun sauke farashin man fetur kasa da yadda Dagote ke sayarwa

Wasu masu shigo da man fetur daga ƙasashen waje sun fara sayar da shi a ƙasa da Naira 860 kowace lita, lamarin da ya sauka...

Saurayi ya gaggabe wa budurwarsa hakora shida a Legas

Wani saurayi a unguwar Ibadan dake Ebute Meta, jihar Legas, ya lakadawa budurwarsa Fatima, wadda ke sana’ar gyaran kai, dukan da ya janyo ta rasa...

Mafi Shahara