DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kashim Shettima ya kaddamar da wasu ayyuka a jigawa, ya kuma bukaci matasa su gujewa shiga zanga-zanga

-

Kashim Shettima ya kaddamar da wasu ayyuka a jigawa, ya kuma bukaci matasa su gujewa shiga zanga-zanga

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ziyarci jihar Jigawa a ranar Talata domin kaddamar da wasu ayyuka da ofishin sa ya jagoranta. A yayin ziyarar tasa, Shettima ya bukaci matasan da su kaurace wa shiga zanga-zanga, inda ya bayyana cewa, ba za ta haifar da ci gaba mai kyau ba, kuma za ta iya haifar da tashin hankali da asarar dukiyoyin jama’a.

Google search engine

Ya jaddada cewa gwamnatin su karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tana aiki tukuru wajen aiwatar da manufofi da shirye-shirye da nufin inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma yabawa gwamna Malam Umar Namadi bisa bullo da tsare-tsare masu da zasu inganta rayuwar al’ummar Jigawa.

Gwamna Namadi ya bayyan ziyarar mataimakin shugaban kasar a matsayin wadda tazo da alheri da amfani mai tarin yawa ga al’ummar jihar Jigawa.

Yace mataimakin Shugaban kasa ya kaddamar da asibitocin MSME don inganta harkokin lafiya, kasuwanci da bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu. Ya kuma kaddamar da shirin noman rani mai amfani da hasken rana mai fadin hekta 20,000.

Sauran ayyukan sun hada da kaddamar da samar da wutar lantarki mai ta hasken rana mai karfin KVA 100 domin samar da tsayayyar wutar lantarki ga masu kananan sana’o’i a kasuwannin Dutse, da kaddamar da shirin horas da matasa 1,000 daga jihar Jigawa kan sabuwar fasahar zamani ta Artificial intelligence (AI).

Gwamna Namadi ya ce mun yi farin ciki da cewa wannan ya yi daidai da ajandarmu ta inganta rayuwar al’ummar Jigawa, inda muke shirin aiwatar da tsare-tsare masu inganci don tallafawa da inganta harkokin kasuwanci, sana’o’i, da bunkasa kananan ‘yan kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kamfanin NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar man birnin Port Harcourt

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya musanta labarin cefanar da matatar mai ta Fatakwal ga yan kasuwa A Yayin wani taro da kamfanin ya gabatar...

Tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa daga 2025 zuwa 2026 – IMF

Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya sabunta hasashensa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ya ce zai kai kashi 3.4 cikin 100 a shekarar...

Mafi Shahara