DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Tinubu ta hannun hukumar NCAOOSCE ta zakulo yara 20,000 domin sanya su a makarantun boko a Abuja

-

 

Hukumar kula da Almajirai da yaran da ba su zuwa makarantun boko a Nijeriya ta sanar da kammala zakulo yara sama da 20,000 domin mayar da su makarantun boko.

An samu wannan jimillar yaran ne bayan wani gagarumin aikin fadakar da jama’a na  makonni uku da jami’an hukumar  NCAOOSCE suka shiga lunguna da sako-sako na babban birnin tarayya, Abuja.

Shugaban hukumar Muhammad Sani Idris ya jinjina wa jami’ansa da ake kira Marshals wadanda aka dora wa alhakin zakulo yaran da ba su zuwa makarantun bokon cikin wani kankanin lokaci.

A cikin wata sanarwa da Malam Nura Muhammad, babban mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga shugaban hukumar ta NCAOOSCE ya fitar, hukumar ta ce  tana da shirin saka milyoyin yara makaranta a duk shekara.

Sanarwar ta ce, da farko an fara kokarin ganin an saka yara 10,000 makaranta, amma irin hobbasar da hukumar ta nuna ya sa aka samu sakamakon da ya ba mutane mamaki.

Muhammad Sani Idris ya ce nan da zuwa watan Satumba, wadannan yara da ake zakulo za a sanya su a makarantun boko dabam-dam da ke yankin Abuja. Ana kuma sa ran daga nan shirin zai fadada zuwa suaran yankunan Nijeriya. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sojojin Nijeriya sun kwato shanu 1,000 daga hannun barayin daji a jihar Taraba

Dakarun runduna ta 6 ta sojin Nijeriya na Operation WHIRL STROKE tare da hadin guiwar dakarun aikin SAFE HAVEN, sun kashe ‘yan bindiga biyu tare...

Shugaba Tinubu ya shiga ganawar sirri da manyan hafsoshin tsaron Nijeriya

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu na wata ganawar sirri tare da shugabannin tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP a fadar shugaban kasa da...

Mafi Shahara