DCL Hausa Radio
Kaitsaye

‘Yan bindiga sun sace matafiya da dama a hanyar Mariga-Kontagora jihar Niger

-

 

Google search engine

Rahotanni daga jihar Niger na cewa masu garkuwa da mutane sun sace akalla fasinjoji 20 da suke a cikin motoci biyar yayin da suke kan hanyar Mariga zuwa Kontagora.

Kakakin majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar mazabar Mariga, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema a ranar Juma’a a garin Minna babban birnin jihar.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis yayin da ‘yan bindiga suka tare hanyar Mariga zuwa Kontagora tsakanin Baban-Lamba da Beri.

Jihar Niger da daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro a Arewacin Nijeriya 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Super Eagles ta fara farfado da burinta na zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026

Hukumar kwallon kafar Nijeriya ta fara dawo da burin zuwa gasar cin kofin duniya ta 2026 Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Najeriya (NFF) ta shigar da ƙorafi...

Dangote ya shigar da ƙorafi ga hukumar ICPC kan shugaban hukumar NMDPRA

Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya shigar da ƙorafi ga Hukumar ICPC yana zargin Shugaban Hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed, da cin hanci da almundahanar kudade. A...

Mafi Shahara