DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An gurfanar da ‘yan kasar waje 113 akan laifukan yanar gizo da shigowa Nijeriya ba bisa ka’ida ba

-

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce ta gurfanar da wasu ‘yan kasar waje 113 da laifukan da suka shafi yanar gizo, wadanda suka hada da zamba da safarar kudade da dai sauran su. 
Wani bayani da mai magana da yawun rundunar ya wallafa a shafinsa na X, Olumuyiwa Adejobi, ya ce ofishin rundunar ‘yan sanda mai yaki da laifukkan yanar gizo ne ya kama mutanen a ranar 3 ga watan Nuwamban 2023 a birnin tarayya Abuja.
Wadanda aka kama a yayin sammen, na fuskantar zarge-zarge ciki har da wadanda suka shafi shige da fice da kuma safarar bil adama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sabbin dokokin haraji za su fara aiki a 1 ga Janairu 2026 — Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki a ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara tun da...

An takaita amfani da kafafen sada zumunta a Guinea

Guinea ta takaita amfani da TikTok, YouTube da Facebook yayin jiran sakamakon zaben shugaban kasa. Gwamnatin Guinea ta takaita shiga shafukan sada zumunta na TikTok, YouTube...

Mafi Shahara