DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Wani abu mai hatsari har biyu ya sake fashewa a Zamfara

-

Akalla ababen fashewa biyu da ‘yan bindiga suka dasa, sun tashi a wuri biyu dake cikin Dansadau a karamar hukumar Maru jihar Zamfara.

Fashewar ta afku ne a kan hanyar Dansadau zuwa Malamawa da kuma hanyar Malele duk a cikin yankin Dansadau bayan da wata motoci su ka taka abin fashewar sai dai babu asarar rayuka.
Zuwa lokacin rubuta wannan labarin, jaridar Premium Times bata samu ji daga mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Zamfara ba saboda lambarsa bata zuwa.
Ko ranar Laraba wani abin fashewa ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12 a karamar hukumar Maru, lamarin da rundunar ‘yan sanda ta ce Lakurawa ne ke kokarin tsallakawa zuwa Dajin Birnin Gwari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rashin tabbas da matsalolin tsaro na barazana ga burin ECOWAS na 2050 – Shugaban ECOWAS, Touray

Shugaban kungiyar ECOWAS, Omar Touray, ya ce rashin tabbas a duniya, matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki na hana kungiyar cimma burinta na Vision 2050,...

An yi ajalin wata mace mai juna biyu da wani karamin yaro a cikin birnin Kano

Al’ummar Sheka Sabuwar Gandu a karamar hukumar Kano Municipal sun shiga firgici a daren Asabar bayan wasu da ba a san ko su waye ba...

Mafi Shahara