Wani sabon rahoton hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya karu zuwa kashi 34.60 a cikin watan Nuwamban da ya gabata.
Rahoton ya nuna cewa an samu karin kashi 0.70 a cikin wata daya, inda a watan Oktoba ma’aunin yake a kashi 33.88.
Hakama kididdiga ta shekara daya ta nuna cewa tashin farashin kayan abinci a watan Nuwamba ya kai kashi 38.67, abinda ke nuna ya karu da kashi 11.58 idan aka kwatanta da shekara ta 2023 da tashin farashin kayan abinci yake kashi 27.09.