DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mutane 3 sun mutu yayin wani rikici a jihar Taraba

-

‘Yan sandan Nijeriya 

Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar mutane uku a wani rikici da ya barke tsakanin mabiya addinin kirista na majami’ar United Methodist da majami’ar Global Methodist a jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, inda ya ce rikicin ya faru ne a karamar hukumar Karim-Lamido tsakanin mabiya majami’un biyu tun a ranar Lahadi.

Google search engine

A cewarsa, rundunar ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a rikicin, yana mai cewa yanzu haka an tura jami’an ‘yan sanda da sojoji domin dakile aukuwar rikicin a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kama Maduro da Amurka ta yi

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro. Ramaphosa ya...

Sojoji sun ceto mutane shida da aka sace a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarar ceto mutane shida da aka sace a wani sumame da suka gudanar a yankunan Kajuru da Kujama...

Mafi Shahara