DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Matatar man Dangote ta rage farashin litar fetur zuwa Naira 899

-

Matatar mai ta Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 899.50 domain saukakawa ‘yan Nijeriya, gabanin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.
A cikin wani bayani da mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejina ya fitar, ya ce kamfanin ya rage farashin ne domin rage musu yawan kudin da za su kashe wurin zirga-zirga.
Ko a watan Nuwamba matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 970 akan kowace lita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawa ta bukaci a dauki matasa aikin tsaro domin magance matsalar tsaro

Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla...

Matukar dimokradiyya ta gaza a Nijeriya sai ya shafi fadin Yammacin Afrika – ECOWAS

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a...

Mafi Shahara