DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Shugaba Tinubu, gwamnoni, shugabannin majalisa, da wasu jagorori sun yi kira da a rungumi zaman lafiya, da hadin kai a yayin bukukuwan Kirsimeti

-

Bola Ahmad Tinubu, Shugaban Nijeriya 

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da gwamnonin kasar da shugabannin majalisa da wasu jagorori sun yi kira da a rungumi son juna, zaman lafiya da kuma hadin kai, a daidai lokacin da mabiya addinin kirista ke bukukuwan Kirsimeti a fadin duniya.
Shugabannin sun kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su yi addu’a ga masu mulkin kasar domin dorewar ci gaban kasar.
Daga cikin wadanda su ka yi wadannan kiraye-kirayen har da kakakin majalisar wakilai Abbas Tajuddeen, mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma gwamnonin Kwara, Gombe, Bauchi da Nasarawa da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

SERAP ta soki gwamnatin Tinubu game da karin fasfo

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar tabbatar da adalci da shugabanci nagari ta bukaci gwamnatin Nijeriya da ta soke ƙarin kuɗin fasfo da hukumar shige da fice...

ADC ta nesanta kanta da Nasiru El-Rufa’i bayan taron jam’iyyar da aka yi tashin hankali a Kaduna

Rikicin siyasa na ƙara kamari a jihar Kaduna bayan jam’iyyar ADC ta nesanta kanta daga wani taron da aka danganta da tsohon gwamnan jihar, Nasir...

Mafi Shahara