![]() |
Dr Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano |
Rahoton Ukashatu Ibrahim Wakili
—————-
Na gwaggo gugar ƙarfe! Na daga cikin irin kirarin da ake yawan yi wa tsohon Gwamnan jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda a wannan Laraba 25 ga watan Disamba ke cika shekaru 75 da haihuwa.
Shin wanene Dr Abdullahi Umar Ganduje?
An haifi Dr Ganduje a ranar 25 ga watan Disambar 1949 a gidan hakimin Ganduje dake cikin karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano, kuma ya yi karatunsa ne tsakanin jihohin Kano da Kaduna da kuma Oyo inda ya mallaki digirin digir-gir wato PhD.
Abdullahi Umar Ganduje ya fara aiki ne a matsayin malamin makaranta a shekara 1975 lokacin da ya ke aikin hidimar kasa NYSC, bayan haka ne ya fara aiki da ma’aikatar ilimi ta jihar Kano. Ganduje ya fara zama Lakcara a kwalejin malamai ta Kano daga bisani ya wuce jami’ar Bayero University inda ya ci gaba da karantarwa.
Shekaru biyar kacal sai ya koma bangaren shugabanci inda ya yi aiki a jihar Kano da hukumar babban birnin tarayya Abuja, ya kuma shafe shekaru 17 a ma’aikatar yana aiki har ya rike mukamin Kantoman karamar hukumar Abaji da kuma Shugaban karamar hukumar Gwagwalada.
Siyasar Abdullahi Umar Ganduje ta soma ne tun a jamhuriya ta biyu inda ya shiga jam’iyyar NPP kuma ya rike mukamin mataimakin sakatare na jihar Kano a 1979 zuwa 1980, Ya yi kwamishinan ayyuka da gidaje a shekara ta 1994 zuwa 1998, kuma a shekarar ne ya shiga jam’iyyar PDP da burin zama gwamnan jihar Kano na farko bayan Nijeriya ta hau tafarkin dimukradiyya.
Sai dai burin na Ganduje bai cika ba amma ya yi nasarar yin takarar tare da tsohon uban gidansa Injiniya Rabi’u Musa Kankwaso a matsayin mataimakin gwamna kuma al’ummar Kano suka zabe su a 1999 zuwa 2003, a wannan lokacin ya kuma saka ido a ma’aikatar kananan hukumomin Kano.
Kafin ya zama gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya rike mukamai a mtakin tarayya a matsayin mai baiwa ministan tsaro shawara a 2003 zuwa 2007, ya zama mamba na hukumar kula da harkokin jiragen sama ta kasa, ya jagoranci hukumar gudarwa ta kwalejin tarayya ta Ado-Ekiti a 2008 hakazalika ya rike mukamin Sakatare hukumar kula da Tafkin Chadi.
A 2011 zuwa 2015 Ganduje da mai gidansa Kankwaso sun sake komawa kujerar Gwamna da Mataimaki inda suka kammala wa’adi na biyu, bayan Kwankwaso ya sauka ne Abdullahi Ganduje ya dare kujerar Gwamnan Kano karkashin inuwar jam’iyyar APC inda ya kayar da Malam Salihu Takai na jam’iyyar PDP.
Karin bayani: Rahoton cikar Ganduje shekaru 75
Mulkin Ganduje na cike da hargitsi da takun saka, domin tun a wa’adi na farko ya raba gari da Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ajiye jar hula wadda ita ce tambarin akidar Kwankwasiyya tare da samar da wata akidar ta Gandujiyya. Haka ma ya shiga takun saka da Sarki Muhammad Sanusi, har bincikensa sai da Ganduje ya sa aka yi kan zargin wadaka da dukiya kafin daga bisani ya sauke shi kan kujerar mulki, bayan yin dokar da ta raba masaurautar Kano gida 4 wadda ta janyo cece-kuce mai zafi a kasar.
A watan Oktoban 2018, Jaridar Daily Nigerian ta saki bidiyo na fallasa da ya nuna wani da ake cewa gwamna Ganduje ne na karbar makudan kudade da ake zargin cin hanci ne ya karba a hannun wani dan kwangila, sai dai kwamishinan yada labaransa a wancan lokacin ya musanta bidiyon da ya ce an kirkira ne. Har kotu Ganduje ya shigar da Jaridar Dailynigerian da kuma mawallafinta Jaafar Jaafar bisa zargin bata masa suna.
Lokacin zaben 2019 Ganduje ya sha da kyar a hannun Abba Kabir Yusuf, sai da aka je zagaye na biyu na zaben gwamnan, sa’annan mai faruwa ta faru Ganduje ya yi nasara, abin da ya yi wa ‘yan kwankasiya ciwo sosai kuma suke zargin magudin zabe aka yi.
Dr Abdullahi Umar Ganduje ya so mataimakinsa Dr Nasir Yusuf Gawuna da Murtala Sulen Garo su gaje kujerar gwamnan Kano, sai dai guguwar ‘yan Kwankwasiyya ta yi tasiri, ta hana shi cimma wannan burin.
Daga an ne dai Ganduje ya koma cin kasuwar sama, a ka ba shi shugabancin jam’iyyar APC ta kasa bayan saukar Abdullahi Adamu a shekarar 2023, kuma ya sha alwashin kwace mulkin jihohin da ke hannun jam’iyyun adawa, farawa da jihar Ondo a zaben watan Nuwamban 2024.