DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Bello Turji tamkar gawa ce ke tafiya – Hedikwatar tsaron Nijeriya

-

Bello Turji 

Google search engine

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta bayyana cikakken ‘yan bindigar nan mai suna Bello Turji, a matsayin gawa ne ke tafiya.

Wannan dai ya biyo bayan barazanar da kasurgumin dan bindigar ya yi na kai farmaki ga al’ummomin jihar Zamfara.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a cikin wani sabon faifan bidiyo da Bello Turji ya saki Turji kalubalantar sojojin Nijeriya, inda ya zarge su da kama ‘yan uwansu tsofaffi tare da neman a sako abokinsa Bako Wurgi da jami’an tsaro ke tsare da shi.

Ya kuma yi barazanar kai hari a sabuwar shekara mai kamawa ta 2025 matukar ba a biya masa bukatunsa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An yanke wa ɗan Najeriya hukuncin ɗaurin shekaru 11 a Amurka kan damfara da ta kai dala miliyan 1.3

Wata kotu a Amurka ta yanke wa wani ɗan Najeriya mai zama a San Gabriel Valley, Abiola Femi Quadri, hukuncin ɗaurin shekara 11 da wata...

Natasha ta sake shan alwashin komawa majalisar dattawa a ranar Talata

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ‘yar Majalisar Dattawa daga jihar Kogi da aka dakatar, ta shigar da ƙara ga Majalisar Dattawa tana neman su girmama hukuncin Babbar...

Mafi Shahara