DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ana zargin wata mata da yin ajalin mijinta ana shirye-shiryen bikin sunan ɗansa

-

 

‘Yan sanda

Google search engine

An kama wata mata mai suna Fatima Dzuma ‘yar kimanin shekaru 27 bisa zargin ta da ajalin mijinta Baba Aliyu mai shekaru 25 a jihar Neja.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Lafiyagi Dzwafu da ke karamar hukumar Katcha ta jihar, a lokacin da ake shirye shiryen bikin nadin sunan dansa da matarsa ta farko ta haifa masa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Abiodun Wasiu, ya ce an kama Fatima ne bayan an gano gawar mijinta a wani daji da ke kusa da gidansu, kwanaki uku bayan an nemeshi an rasa.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, kakakin ‘yan sandan ya ce wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumar ta da shi, inda ta ce a lokacin da mijin ta yake barci ta halaka shi, sannan ta daure shi da igiya kafin ta jefar da gawar a cikin daji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ma’aikatar tsaron Nijeriya na bukatar ƙwararren shugaba – Shehu Sani

Tsohon dan majalisar dattawan Nijeriya da ya wakilci Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya nuna bukatar samun ƙwararren shugaba da zai jagoranci ma'aikatar tsaron...

Wike na rikewa Tinubu duk filin da gwamnati ta kwace a Abuja – Hadiminsa

Hadimi ga ministan Abuja Nyesom Wike, Lere Olayinka ya bayyana cewa duk wani fili da gwamnati ta kwace iko da mallakarsa a birnin na kasancewa...

Mafi Shahara