DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsoma baki da manyan arewa ke yi wajen tsayar da ɗan takara ci baya ne ga dimukradiyya – Kwankwaso

-

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi wasu mutane da yace na ayyana kan su a matsayin jagororin arewa da yin katsalandan a sha’anin zaben dan takarar shugabancin kasa.
A zantawarsa da BBC Hausa, jagoran darikar Kwankwasiyya, ya yi zargin cewa hakan na kawo ci baya ga dimukradiyyar kasar tare da raba kan al’umma har ta kai ga an zabi dan takarar da bai cancanta ba.
Kwankwaso kuma tsohon gwamnan Kano ya jaddada bukatar jagororin su dauki darasi daga abubuwan da suka faru a baya tare da tsame bakinsu a duk wani sha’ani na zaben dan takara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Eng Faruk Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar NMDPRA

Shugaba Tinubu ya bukaci majalisa ta sahale masa nada sabbin shugabannin hukumomin kula da man fetur bayan da Injiniya Farouk Ahmed, ya yi murabus a...

FIFA ta sanya $60 a matsayin kudin tikitin kallon kofin duniya na 2026

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ƙaddamar da sabon rukuni na tikiti a dalar Amurka 60 ga kowane ɗayan wasannin 104 na Gasar Kofin...

Mafi Shahara