DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnan Bauchi ya bai wa ma’aikacin DW Hausa mukamin kwamishina

-

 

Usman Shehu Usman

A wani ci gaban fasaha, majalisar dokokin jihar Bauchi ta kafa tarihi, inda ta tantance mutum na farko da gwamnan jihar ya tura da sunan sa a matsayin kwamishina, Usman Usman Shehu, ta bidiyo ta manhajar Zoom.

Google search engine

Wannan ya nuna kudurin majalisar dokokin jihar na rungumar sabon tsari a cikin al’amuranta, da tabbatar da rungumar fasahar zamani cikin ayyukanta.

Usman Usman Shehu, wanda dan karamar hukumar Giade ne ta jihar Bauchi, ya fara karatunsa na farko da karatun Islamiyya kafin ya wuce makarantar firamare da sakandare a jihar. Ya ci gaba da neman ilimi har zuwa jami’a a yanzu yana zaune a kasar Jamus. Kwararran dan jaridar ya yi shekaru wajen 18 yana aiki da rediyon Jamus a matsayin babban edita.

Duk da an yi tantancewar ta hanyar Zoom a majalisar, amma ba a samu wata matsala ba, inda mambobin majalisar suka yi tambayoyi masu muhimmanci tare da samun ingantacciyar amsa daga Usman Usman Shehu.

Kawo yanzu ba a bayyana ma’aikatar da gwamnan na Bauchi zai tura sabon kwamishinan ba. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalori ya karbi ragamar jagorancin jam’iyyar APC a hukumance

Shugaban riko na jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya bukaci shugabanni da mambobin jam’iyyar da su zauna cikin hadin kai bayan murabus din tsohon shugaban...

An dakatar da jirgin Rano Air kan zargin matsalar inji – NCAA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da wani jirgin Rano Air mai lamba 5N-BZY bayan fuskantar hatsarin gobara da matsalar...

Mafi Shahara