DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar sadarwa NCC ta umarci kamfanonin sadarwa su katse lambobin USSD na wasu bankuna

-

Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, ta umarci kamfanonin sadarwa da su katse lambobin aike sakonnin USSD na bankuna 9, a kasar sakamakon tarin bashin da ake bin su.

Hukumar ta tabbatar da hakan ne ta cikin sanarwar da jami’in yada labaran ma’aikatar ta NCC Rueben Muoka ya fitar a ranar Talata.
Hukumar ta ce ya yin da wasu bankunan suka biya bashin da ake bin su yanzu haka ana bin wasu kudaden da suka zarta sama da biliyan 200.
NCC ta ce ya zama wajibi Bankunan su biya basukan da ake binsu zuwa ranar 27 ga Janairun 2025; ko su rasa manhajar sakonnin ta USSD gaba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Jihohin APC sun sake mara wa Tinubu baya matsayin dan takara a zaɓen 2027

Jam’iyyar APC a jihohi da dama ta sake bayyana goyon bayanta ga shugaba Bola Tinubu, a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben...

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Mafi Shahara