DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Iconic Open University ta sanar da ranakun jarabawar Zangon karatun 2024/2025

-

 

Daliban Iconic Open University Za Su Yi Jarabawa A Cibiyoyi 57 a Nijeriya Da Kuma 11 A Kasashen Waje 

Google search engine

Jami’ar Iconic mai gabatar da tsarin karatu na tafi-da-gidan ka (open and distance learning) wadda keda sahalewar hukumar NUC a Najeriya za ta fara jarabar karshen zangon karatu 2024/2025 a ranar Litinin 20 ga watan Janairu 2025 a cibiyoyi 57 a fadin Najeriya da kuma 11 a kasashen ketare da suka hada Amurka, Birtaniya, Saudiyya, Iran, Canada, Algeria, Misira, Africa ta Kudu, Ghana da Kasar Qatar domin baiwa dalibai damar gabatarda jarabawar a garuruwan da suke zaune. 

Magatakardar jami’ar Malam Muhammad G. Sanusi ne ya sanar da hakan ga manema labarai a madadin shugaban gudanarwar jami’ar. Ya jaddada shiri na mussaman da jami’ar tayi domin gabatar da jarabawar cikin nasara ga duk bangaroran dalibai na matakin digirin  farko dana biyu. 

Wannan ya kara tabbatar da burin jami’ar na isar da ilimin a duk lungu da sakon da dalibai suke, domin cimma gurin ta na tsarin tafi-da-gidan ka dai dai da karni na ashirin da daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ramaphosa ya yi Allah-wadai da kama Maduro da Amurka ta yi

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta ɗauka na kama Shugaban ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro. Ramaphosa ya...

Sojoji sun ceto mutane shida da aka sace a Kaduna

Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun samu nasarar ceto mutane shida da aka sace a wani sumame da suka gudanar a yankunan Kajuru da Kujama...

Mafi Shahara