DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar tace finafinai ta haramta wa Usman Sojaboy da wasu mata biyu shiga harkokin fim ko waka a jihar Kano

-

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da Usman Sojaboy mawaki a Kannywood da wasu jarumai biyu Shamsiyya Muhammad da Hasina Suzan daga shiga duk wasu harkoki na Kannywood a Kano.

An yanke wannan hukuncin ne bayan wani faifan bidiyo da ya bayyana da ke nuna wasu dabi’u da ya sabawa addini, al’ada da dabi’un musulmi. A cewar hukumar ta samu korafe-korafe da dama daga al’umma da kuma malaman jihar.

Google search engine

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in yada labaran hukumar Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana cewa an sha gargadin Sojaboy akan abubuwa irin wa’yanda suka saba da tarbiyya da al’ada.

Sanarwar ta ce babban sakatare a hukumar tace fina-finan ta Kano,Abba El-Mustapha ya umurci sashin tantancewa da su tabbatar da cewa Sojaboy da jaruman biyu ba su shiga cikin wani shiri da ake a Kannywood ba,ya ce hukumar ba za ta lamunci duk wani abu da ya sabawa tarbiyya ko al’ada ba don haka ta dakatar da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnan Bauchi ya sanya hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu 13 a fadin jihar

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya sanya hannu kan dokar kirkirar sabbin masarautu 13 a fadin jihar. Daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin da yake sanya...

Kenya da Senegal sun kulla yarjejeniyar shige da fice ba tare da biza ba

Gwamnatocin Kenya da Senegal sun bai wa juna damar shige da fice ga 'yan kasashensu ba tare da biza ba na tsawon kwanaki 90. DW Africa...

Mafi Shahara