DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jiragen yaki sun yi luguden wuta tare da ajalin ‘yan ta’adda da dama a jihar Neja

-

Wani farmaki da jiragen rundunar sojin saman Nijeriya suka kai a maboyar ‘yan ta’adda ya yi sanadiyar mutuwar wadanda ake zargin ‘yan bindiga da dama a dajin Alawa Forest cikin karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Rundunar ta ce an kai harin ne karkashin rundunar Operation Fansan Yamma dake yaki da ‘yan bindiga a yankin Arewa ta Yamma da Arewa ta Tsakiyar Nijeriya.
Sanarwar da daraktan yada labarai na ofishin rundunar sojin saman Olusola Akinboyewa, tace an tarwatsa maboyar ‘yan bindigar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar...

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Mafi Shahara