DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Likitocin da ke yajin aiki a Abuja sun ƙalubalanci Minista Wike da Sanata Akpabio su je asibitin gwamnati a duba su

-

Kungiyar lokitoci dake yajin aiki a babban birnin tarayya Nijeriya sun ƙalubalanci Ministan Abuja Nyesom Wike da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da su je asibitocin gwamnati domin a duba su kuma su gane wa kansu irin wahalar da jami’an kiwon lafiya da marasa lafiya ke sha.
Da yake zanta wa da gidan talabijin na Channels, shugaban kungiyar likitocin George Ebong, yace idan har manyan ƙasar nan ba su amfani da asibitocin gwamnati to ba za ayi gyara a fannin kiwon lafiya ba.
A wannan Laraba ne dai likitocin suka soma yajin aikin gargadi na kwana uku saboda kin biyan albashi da alawus alawus dinsu da dai sauran bukatu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

NAHCON ta gargadi maniyyata Hajjin 2026 na Nijeriya kan yin rijista da wuri

By Fatima Aminu Dabo Hukumar jin daɗin alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da jadawalin aikin Hajjin 2026, inda ta bayyana cewa 20 ga Maris, 2026...

Ana ci gaba da neman wata dattijuwa bayan kifewar kwale-kwale dauke da fasinja 11 a Sokoto

An gano gawar wani matashi mai shekara 29 da ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Jihar Sokoto.Lamarin ya faru...

Mafi Shahara