DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya na da isassun kuɗin da Shugaba Tinubu zai yi tafiye-tafiye kasashen duniya – Ministan harkokin waje

-

Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Yusuf Tuggar, ya ce Nijeriya na da isassun kuɗin da za ta iya daukar nauyin tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa kasashen ketare.

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa da gidan talabijin na Channels ke gabatarwa.

Google search engine

Wasu ‘yan Nijeriya dai na yin guna-guni kan yadda shugaban kasar ke yin balaguro daga kasa zuwa kasa, ba tare da kasar ta samu wani ci gaba ba.

Sai dai Ministan ya yi watsi da wannan, inda yace ziyarar shugaban ta jawo wa Nijeriya masu zuba hannun jari da suka saka dala biliyan 2 bayan ziyarar da ya kai a ƙasar Brazil.

Tun bayan hawa karagar mulki a shekarar 2023, rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya ziyarci kasashe kusan 19 a tafiye-tafiye 32 kasashen ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu zai nada jakadun Nijeriya a kasashen wajen

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu na shirin kammala nadin jakadun da za su wakilci Nijeriya a kasashen waje bayan tsawon lokaci kasar na fama da gibi...

Real Madrid na da shiga rai amma burina yin nasara tare da Arsenal – William Saliba

Dan wasan baya na Arsenal, William Saliba, ya bayyana cewa sha’awar da Real Madrid ta nuna masa na da matukar daukar hankali, amma burinsa shi...

Mafi Shahara