DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta ayyana kujerar wani dan majalisa a matsayin babu kowa a kanta, saboda rashin halartar zaman majalisar

-

Google search engine
Majalisar dokokin jihar Zamfara ta ayyana kujerar dan majalisa mai wakiltar Talatar Mafara ta Kudu Aliyu Kagara, a matsayin babu kowa a kanta saboda rashin halartar zaman majalisa a lokaci daban-daban.
Wata sanarwa da sakataren yada labarai na majalisar Bello Kurya ya fitar, ta ce an dauki matakin ne saboda cikin zama 180 da majalisar tayi, sau 21 kawai dan majalisar ya halarci majalisar.
Sanarwar ta ce hakan ya saba wa kundin tsarin mulki na Nijeriya kuma majalisar ta nada kwamitocin domin zama da dan majalisar amma abin ya ci tura.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan bindiga sun hallaka manoma 32 a jihar Niger

Akalla manoma 32 ne aka hallaka a hare-haren da ’yan bindiga suka kai kan al’ummomin Tugan-Makeri, Konsoko da Pissa a karamar hukumar Borgu ta Jihar...

Peter Obi ya bukaci matasa da su nuna kauna da kishin Nijeriya albarkacin ranar masoya

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya, Peter Obi, ya bukaci ’yan Nijeriya musamman matasa su yi bikin ranar masoya ta Valentine cikin nuna kishin ƙasa da...

Mafi Shahara