Tsohon kakakin majalisar wakilai ta Najeriya Yakubu Dogara, ya zargi gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da cin amanar ministan birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike.
Ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Dogara ya bayyana cewa Wike ya taka gagarumar rawa wajen nasarar Sanata Bala Muhammad gwamnan jihar Bauchi a shekarar 2019.
Dogara ya bayyana yadda Wike ya umarci shugaban gudanar da zaben ‘yan takara na PDP a wancan lokacin Dan Orbih ya tabbatar da samun nasarar Bala Muhammad kan abokin karawarsa a Sanata Abdul Ningi.