DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Tsaro da tattalin arziki sun inganta a lokacin ina shugaban Nijeriya – Muhammad Buhari

-

Google search engine

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tsaro da tattalin arzikin kasar nan sun inganta sosai a tsawon shekaru takwas da yayi yana mulki.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina a gidan sa dake Daura a jihar Katsina.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ya gaji mummunar tattalin arziki da kalubalen tsaro daga jam’iyyar PDP da ta shafe shekaru 16 tana mulki.

Buhari, ya tabbatar da cewa dabarun gwamnatinsa sun yi nasarar magance wadannan kalubale, wajen dakile ta’addanci da matsalolin tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sojoji sun amince an kitsa yunkurin juyin mulki kan Tinubu

Rundunar sojin Najeriya ta amince cewa wasu jami’anta sun kitsa yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne...

Hukumar ‘yansandan Nijeriya ta tsawaita wa’adin daukar jami’ai aiki

Hukumar Kula da ayyukan ‘yansandan Nijeriya (PSC) tare da rundunar ‘yansandan sun tsawaita wa’adin ɗaukar sabbin 'constable' guda 50,000 da makonni biyu, bayan da aka...

Mafi Shahara