DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An kori daliba ‘yar TikTok da ta ci kwalar lakcara a jami’ar UNIZIK da ke Anambra

-


Mahukuntan jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Awka jihar Anambra sun kori dalibar nan Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, bisa cin kwalar wani malami tare da kama shi da fada saboda ya wuce a cikin bidiyon TikTok da take yi.
A cikin wasikar kora mai kwanan watan 13 ga watan Fabrairu 2025, dauke da sa hannun mukaddashin magatakardar makarantan Victor I. Modebelu, jami’ar ta ce dabi’un dalibar sun saba wa dokokin makarantar.
Lamarin dai ya dauki hankali sosai a cikin shafukan sada zumunta, bayan da bidiyon da dalibar da malaminta ya bayyana.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamnatin Nijeriya ta bukaci sabon shugaban hukumar kula da gidajen gyaran hali ya mayar da hankali wajen sauya tunanin daurarru

Gwamnatin tarayya ta bukaci sabon shugaban hukumar kula da gidajen ajiya da gyaran hali na kasar Sylvester Nwakuchi, da ya mayar da hankali wajen sauya...

ECOWAS ta yi kira ga Nijar, Mali da Burkina Faso su sake shiga kungiyar

Majalisar kungiyar kasashen yammacin Africa wato ECOWAS ta yi kira ga kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar da su sake nazari kan matakin ficewar cikin...

Mafi Shahara