DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Saboda dalilai na sirri ba za mu fadi dalilin hana wa sojojin Nijeriya visa ba – Ofishin jakadancin Kanada

-

Ofishin jakadancin kasar Kanada a Nijeriya ya ce ya yanke shawarar kin bayani akan dalilin da ya sa aka hana wa babban hafsan sojoji Janar Christopher Musa visa da wasu manyan sojoji saboda dalilai na sirri.
Sai dai a martanin ministan cikin gida na Nijeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya ce babu dalilin da gwamnatin kasar za ta hana wa sojojin izinin shiga kasar.
Hakama mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana matakin a matsayin cin fuska ga Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yansanda sun dakile yunkurin ‘yan bindiga na tare wata babbar hanya a Zamfara

Rundunar Ć´ansandan jihar Zamfara ta bayyana samun nasarar dakile wani yunkuri daga 'yan bindiga na tare wata babbar hanya.   Wata sanarwa da mai magana da yawun...

Ni ne dan siyasa na biyu da aka fi ci wa zarafi a Nijeriya – Nyesom Wike

Ministan Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa shi ne dan siyasa na biyu da aka fi ci wa zarafi a Nijeriya bayan shugaban kasa Bola...

Mafi Shahara