DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar wakilan Nijeriya za ta gayyaci shugaban hukumar zabe INEC kan jinkirin gudanar da zaben cike gurbi na ‘yan majalisar tarayya da na jihohi

-

 

Farfesa Mahmood Yakubu

Google search engine

Majalisar wakilan Nijeriya ta umurci kwamitinta mai kula da harkokin zabe da ya gayyaci shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmood Yakubu da ya gurfana a gabanta domin bayyana dalilan da ya janyo jinkirin gudanar da zaben cike gurbi na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi.

Majalisar ta cimma matsayar ne yayin zamanta na ranar Talata bayan amincewa da kudirin da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa a jihar Bauchi, Jafaru Leko ya gabatar.

Da yake magana kan sashe na 68 na kundin tsarin mulki wanda akai wa kwaskwarima a 1999, dan majalisar ya ce tilas ne a bayyana kujerun wa’yanda za su sake zabe da wa’yanda suka mutu a matsayin ba kowa akai, yana mai jaddada cewa sashe na 76(2) cikin baka ya tanadi gudanar da zaben cike gurbi bayan wata daya da samun gurbin da aka rasa ko ake bukatar sake zabe a wasu akwatunan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsare-tsaren Tinubu na farfaɗo da martabar Nijeriya a duniya -Kashim Shatima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na sake gina martabar Nijeriya a idon duniya tare...

Gwamnatin Nijeriya na shirin dakatar da shigo da kayan tsaro daga waje

Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa. Minista a ma'aikatar Tsaron...

Mafi Shahara