DCL Hausa Radio
Kaitsaye

IPMAN ta yi barazanar shiga yajin aiki kan rashin biyan ta bashin Naira biliyan 100 a Nijeriya

-

 

Google search engine

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta a Nijeriya ta yi barazanar rufe gidajen man fetur a fadin kasar nan da sati daya idan hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa NMDPRA ta gaza biyan mambobinsu Naira biliyan 100 na alawus-alawus ga hukumar.

Wannan dai na a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ga manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Shugaban kungiyar Yahaya Alhassan, ya bayyana matukar takaicinsa kan abin da ya bayyana a matsayin sakaci da gangan da hukumar NMDPRA ta yi, duk kuwa da alkawuran da ta sha yi na warware basussukan.

A cewar Yahaya Alhassan, NMDPRA ta tabbatar wa IPMAN a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da kungiyar masu motocin haya ta Najeriya NARTO, ta shirya cewa za ta biya kudaden a cikin kwanaki 40.

Ya kara da cewa yan kasuwan mai na cikin mawuyacin hali sakamakon rashin biyan su hakkokinsu.

Shugaban ya ce jinkirin rashin biyan alawus din ya gurgunta ayyuka a depots na Arewa guda tara da suka hada da Jos, Gusau, Minna, Suleja, Kaduna, Kano, Gombe, Yola, da Maiduguri.

Kungiyar ta kuma nuna rashin jin dadin ta kan harajin kashi biyar cikin 100 da NMDPRA ta dorawa mambobinta idan za’a sayar da gidajen man fetur, wanda suka bayyana a matsayin wanda ya sabawa tsarin mulki da ci gaban kasa.

“Ba za mu yi jinkirin daukar matakai ba idan har ba a biya mu bukatunmu ba daga yau Litinin 24 ga Fabrairu, 2025.

“Idan ba su biya mana kudaden mu ba nan da kwanaki bakwai, za mu da katar da ayyukanmu a duk fadin Nijeriya”.

Kungiyar ta IPMAN ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya shiga tsakani kan takaddamar da ta ki ci taki cinyewa, ta kuma bukaci mambobinta da su jajirce wajen bin doka da oda yayin da suke jiran a biya su hakkokinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Buhari mutum ne mai girmama al’adu da masarautu – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya shiga sahun wadanda ke jimamin rasuwar tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti a...

An rufe ofishin jakadancin Amurka na Abuja da Legas don jimamin rasuwat Buhari

Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja da kuma na Legas za su kasance a rufe a ranar Talata, 15 ga Yuli, 2025, domin girmamawa da...

Mafi Shahara