DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An ba ‘yan makarantun boko hutun azumi a jihar Kano

-

 

Abba Kabir Yusuf

Google search engine

Gwamnatin jihar Kano ta amince da ranar Juma’a 28 ga Fabrairu, 2025, a matsayin ranar fara hutun zango na biyu a makarantun Firamare da na Sakandire a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar, Balarabe Kiru ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce daliban makarantun kwana za su koma makarantunsu a ranar Lahadi, 6 ga Afrilu, 2025 yayin da za a ci gaba da karatu a ranar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025.

Sai dai sanarwar ta ruwaito Kwamishinan ilimi,Ali Haruna Makoda, yana kira ga iyaye da su kula da ‘ya’yansu a lokacin da ake hutun kuma su tabbatar da bin ka’idojin ranar da za a koma makarantu.

Ya yi gargadin cewa za a dau matakin ladabtarwa a kan daliban da suka ki bin ka’ida ta komawa makaranta bayan karewar kwanakin hutun.

Makoda ya yaba da hadin kai da goyon baya da ake bai wa ma’aikatar tare da yi wa dalibai fatan samun nasarar azumin watan Ramadan ba tare da wata matsala ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Muna biyan ‘yan bindiga Naira miliyan 7 don zama a gidajenmu ko noma gonakinmu

Wasu al’ummomi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja sun bayyana cewa suna biyan haraji ga ‘yan bindiga domin su samu damar zama a garuruwansu...

Abin takaici ne a ce tawagar Super Eagles na bin bashi – Peter Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023 Peter Obi, ya bayyana takaici kan rahotannin da ke nuna cewa tawagar wasan...

Mafi Shahara