DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotun Gabon ta yi watsi da takardun takara 19

-

  

Google search engine

Takardun ‘yan takarar shugaban kasa a Gabon hudu ne kotun tsarin mulkin kasar ta amince da su cikin 23 da suka ajiye takardun nuna bukatar yin takarar shugaban kasar a zabe mai zuwa na ranar 12 ga watan Aprilun nan mai kamawa 

Kotun ta ce wadanda aka yi watsi da takardun nasu suna da sa’o’i 72 domin daukaka kara a gaban kotu 

Cikin wadanda kuma aka yi watsi da takardun nasu har da fitaccen dan gwagwarmayar farar hula na kasar Jean-Rémy Yama sakamakon zargin shi da rashin saka takardar haihuwar mahaifin shi 

Daga cikin wadanda aka amince da takardar takarar tasu akwai shugaban gwamnatin rikon kwaryar mulkin sojan kasar Brice Clotaire Oligui Nguema da kuma Alain-Claude Bilie By Nze tsohon Firaministan hambararren shugaban kasar Ali Bongo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Har yanzu bamu kammala bincike ba shiyasa bamu gurfanar da El-rufa’i a gaban kotu ba – EFCC

Hukumar EFCC, mai yaki a cin hanci da rashawa a Nijeriya ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba ta kai tsohon gwamnan Kaduna,...

Wanene sabon Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, Olatunji Disu?

AIG Olatunji Disu ya kasance gogaggen jami’i wanda aka nada don jagorantar rundunar 'yan sandan kasar a matsayin IGP na 23. A cewar fadar shugaban...

Mafi Shahara