DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hadimin Bafarawa ya musanta cewa tsohon gwamnan Sokoton ya koma jam’iyyar SDP.

-

Attahiru Bafarawa

Wani babban hadimin tsohon gwamnan jihar Sokoto,Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya musanta batun sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP.

Google search engine

Mataimakin ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar Punch a Sokoto ranar Talata.

Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa a ranar Talatar da ta anyi ta yada labari a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan ya koma zuwa jam’iyyar SDP.

Idan dai za a iya tunawa, tsohon gwamnan a lokacin da yake bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP a karshen shekarar da ta gabata, ya ce ya yi hakanne domin ya fi mayar da hankali kan sauran manufofin ci gaban Arewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ya kamata Nijeriya ta farka daga barcin da take yi saboda barazanar da Trump ya yi mata – Bishop Kukah

Shugaban Cocin Katolika a Sokoto Archbishop Matthew Kukah ya bayyana cewa barazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan yiwuwar kai harin ga Nijeriya a matsayin nuni...

Wata dattijuwa ta barke da kuka bayan an hanata kada kuri’a

Wata datijuwa mai shekaru 96 a duniya, Mrs. Elizabeth Onike, ta barke da kuka a rumfar zaɓe saboda an hana ta kada kuri'a a Anambara Dattijuwar...

Mafi Shahara