DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Manchester United ta bayyana shirin ta na gina sabon filin wasa mai daukar ‘yan kallo a kujerun zama 100,000

-

Old Traford

Manchester United ta sanar da shirin gina sabon filin wasa mai daukar mutane 100,000 wanda days daga cikin mamallaka kungiyar Jim Ratcliffe ya ce zai zama filin wasan kwallon kafa mafi girma a duniya.

Kungiyar da ke buga gasar Premier ta kasar Ingila ta yi nazarin ko za ta sake gina filin ta na Old Trafford mai tarihi ko kuma gina sabon filin wasa a yankin.

Sai dai a yanzu United din ta tabbatar da aniyyar ta na gina sabon filin wasa mai kujerun zama 100,000 a matsayin sabuwar Old Trafford.

An samar ds hotuna na yadda sabuwar Old Trafford da kewaye za ta kasance a ranar Talata a hedkwatar gine-ginen Foster + Partners na London, wanda aka nada a watan Satumba don tsara filayen wasanni.

Manchester Uniter ta ce filin na Old Traford anyi aiki da shi acikin shekaru 115 da suka gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

An saki ‘Yan jaridar Sahara FM da aka tsare a Agadez

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an saki ‘yan jarida uku na gidan rediyon Sahara FM da ke Agadez bayan da aka tsare su...

Kwamishinan Jigawa ya mayar da rarar Naira miliyan 301 daga kudaden da aka ware don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya mayar da Naira miliyan 301 zuwa baitul malin jihar, daga cikin Naira biliyan...

Mafi Shahara