Dan shugaban kasa Bola Tinubu Seyi Tinubu, ya ce mahaifinsa ne kadai shugaban kasa da bai yi yunkurin wadata kansa ba da dukiyar kasa.
Ya bayyana haka ne a ‘yan kwanan nan, yayin da yake jawabi ga matasa a Yola jihar Adamawa.
Seyi, wanda ke rangadin jihohin arewa domin buda bakin da matasa a azumin watan Ramadan, ya ce mutane na sukar ahalinsa amma duk da haka, mahaifinsa ya jajirce wajen ganin ci gaban Najeriya.