Majalisar dokokin jihar Ribas ta fara shirin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakinsa Farfesa Ngozi Odu bisa zargin aikata ba dai dai ba.
Gidan talabijin na AIT ya ruwaito cewa, majalisar ta umurci akawunta da ya wallafa zarge-zargen da ake yi wa Gwamna Sim Fubara da mataimakinsa, Farfesa Ngozi Odu a jaridu, kamar yadda sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ya tanada.


