Hukumar kare yaduwar cututtuka ta Nijeriya NCDC ta nuna damuwar game da karuwar kamuwa da cutar sankarau a kasar, wadda ta haddasa mutuwar mutane 74 a fadin jihohi 22 na kasar.
Darakta Janar na hukumar NCDC, Dr Jide Idris ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Nijeriya ranar Litinin a Abuja.
Idris ya ce hukumar ta dauki matakin gaggawa ta hanyar tura jami’anta musamman a jihohin Kebbi, Katsina, da Sokoto, wadanda aka fi samun bullar cutar.




