Gwamna jihar Edo Monday Okpebholo ya kai ziyarar jaje ga mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin bisa hallaka matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a makon da ya gabata.
Mataimaki na musamman ga Sanata Barau kan harkokin yada labarai Alhaji Ismail Mudashir, ya ce gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga mataimakin shugaban majalisar, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar Edo za ta taimaka wa iyalan wadanda lamarin ya shafa.
Gwamnan jihar Edo ya bayyana cewa mutane 14 da ake zargi da hannu a kashe matafiyan da ba su ji ba ba su gani ba, ana shirin kai su a Abuja domin ci gaba da yi musu tambayoyi.