DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Sanata Barau ya gana da gwamnan Edo kan hallaka matafiya a Uromi, yayin da ake shirin tura wadanda aka kama zuwa Abuja

-

 

Google search engine

Gwamna jihar Edo Monday Okpebholo ya kai ziyarar jaje ga mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin bisa hallaka matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a makon da ya gabata.

Mataimaki na musamman ga Sanata Barau kan harkokin yada labarai Alhaji Ismail Mudashir, ya ce gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga mataimakin shugaban majalisar, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar Edo za ta taimaka wa iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Gwamnan jihar Edo ya bayyana cewa mutane 14 da ake zargi da hannu a kashe matafiyan da ba su ji ba ba su gani ba, ana shirin kai su a Abuja domin ci gaba da yi musu tambayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar wakilan Nijeriya ta umarci a duba tare da sake fitar da dokokin haraji

Majalisar Wakilai a Nijeriya ta ce ta fara duba dokokin gyaran haraji bayan korafe-korafen jama’a da zargin an sauya wasu sassan dokokin da aka riga...

Amurka ta yabawa gwamnatin Nijeriya bayan kaddamar da hari

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin Najeriya bisa goyon bayan da ta bayar a yayin farmakin sama da aka kai kan...

Mafi Shahara