Wata babbar kotu a jihar Bayelsa ta bayar da umurnin hana magoya bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike gudanar da gangami a jihar har sai ta saurari karar da aka shigar a gabanta.
An dai shirya taron gangamin ne a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa, a ranar 12 ga Afrilu, 2025.
Alkalin kotun mai shari’a I. A Uzakah ya amince da bukatar da babban lauyan jihar ta Bayelsa Biriyai Dambo (SAN) ya shigar tare da dage sauraron karar zuwa 11 ga Afrilun 2025.