Tarihin rayuwar marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi

-

 

A cikin wasiyyar da Marigayi Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya bari ya haramta daukar hoto a wajen jana’izarsa, ya hana taron amsar gaisuwa a gidansa, ya kuma hana mutane shiga makabartar da takalmi a yayin da za a kai shi makwancinsa.

Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, fitaccen malamin addinin Musulunci daga jihar Bauchin Nijeriya. An haife shi ne a garin Gwaram dake karamar hukumar Alkaleri, kuma ya yi rayuwarsa ne tsakanin jihohin Bauchi, Gombe da Nasarawa.

Ya yi karatu a College of Education, Legal and General Studies Misau, jihar Bauchi da kuma Bayero University Kano.

Dr Idris ya fara karatun degree a Jamhuriyar Nijar kafin daga bisani ya wuce kasar Saudiyya inda ya karanci fannin shari’ar Musulunci a jami’ar Madina.

Bayan ya dawo ne ya fara karantarwa a jihar Bauchi, yana tsaka da karantarwar kuma ya wuce Jami’ar Plateau inda ya yi digiri na biyu wato Masters dinsa.

Haka zalika Malamin ya yi karatun digirin digirgir na PhD a kasar Sudan a fannin Usulul Fiqh sai kuma ya tsunduma karantarwa.

Sanannen malamin ya yi fice wajen tsayuwa kan koyarwar addini, tare da tsauri a cikin wa’azozinsa.

A baya-bayan nan, an samu takun saka tsakaninsa da hukumomin jihar Bauchi, wanda ya kai ga cafke shi tare da gurfanar da shi a kotu bisa zargin haddasa fitina da tayar da tarzoma, kafin bayar da belinsa cikinwatan Mayun 2023 bayan shafe wani lokaci a gidan yari. 

Baya ga karantarwa, Dr. Idris kuma dan kasuwa ne, kamar yadda ya bayyana a wata hira da yayi da gidan rediyon Globe FM Bauchi.

Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya bar tarihi mai cike da koyi da jajircewa wajen yada ilimin addinin Musulunci da kuma tsayuwa kan gaskiya, duk da kalubalen da ya fuskanta a rayuwarsa.

An dade ana kwatanta Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi da marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya – fitaccen malami da ya rayu da koyarwar da ta sha bambam da ra’ayin yawancin manyan malaman Izala na lokacinsa.

Sheikh Albani da Dr. Idris sun yi fice wajen caccakar abubuwan da suka sabawa Sunnah, ko da kuwa daga cikin malaman Izala ne ko wasu kungiyoyi. 

Dukansu sun samu horo daga manyan makarantu na Ć™asashen Saudiyya. 

Dr. Idris na daya daga cikin malamai da suka yi mukabala tare da shugaban kungiyar Boko Haram Muhammad Yusuf.

Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ya auri mata hudu, yayin da ya haifi ‘ya’ya sama da talatin da jikoki da dama.

DCL Hausa

Faruk Kafin Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara