DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Bai kamata jami’o’in Nijeriya su rika karrama marasa ilimi da halaye na kwarai ba – Farfesa Jega

-

Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana damuwarsa kan yawan jami’o’in Najeriya da ke ba da digirin kwarewa ga wasu mutane da ya bayyana su a matsayin marasa ilimi ko kuma wadanda ba su da kyakkyawar halayya.
Jega ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro a bikin yaye dalibai karo na 14 na jami’ar NOUN a Abuja. Ya ce wannan dabi’a ta ba da digiri ba tare da la’akari da cancantar ilimi da kyawawan dabi’u ba, tana haifar da koma baya ga darajar digirorin da jami’o’in Najeriya ke bayarwa.
Farfesan ya bukaci jami’o’in Najeriya da su zama masu lura sosai wajen zaben wadanda za a ba da digiri na kwarewa, yana mai gargadin cewa wannan dabi’a na iya rage darajar wannan lambar yabo a cikin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

SGF George Akume ya angwance da tsohuwar matar Ooni na Ife Gimbiya Zainab

Sakataren Gwamnatin Nijeriya (SGF), Sanata George Akume, ya auri Sarauniya Zaynab Ngohemba, tsohuwar matar Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi.   Jaridar Punch ta ce an...

Jirgin yakin Nijeriya da aka tsare a Burkina Faso ya isa Portugal

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya ta tabbatar da cewa jirgin ta kirar C-130 mai lamba NAF 913 ya isa cibiyar gyara jirage ta OGMA da...

Mafi Shahara