Tsohon Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana damuwarsa kan yawan jami’o’in Najeriya da ke ba da digirin kwarewa ga wasu mutane da ya bayyana su a matsayin marasa ilimi ko kuma wadanda ba su da kyakkyawar halayya.
Jega ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi a matsayin shugaban taro a bikin yaye dalibai karo na 14 na jami’ar NOUN a Abuja. Ya ce wannan dabi’a ta ba da digiri ba tare da la’akari da cancantar ilimi da kyawawan dabi’u ba, tana haifar da koma baya ga darajar digirorin da jami’o’in Najeriya ke bayarwa.
Farfesan ya bukaci jami’o’in Najeriya da su zama masu lura sosai wajen zaben wadanda za a ba da digiri na kwarewa, yana mai gargadin cewa wannan dabi’a na iya rage darajar wannan lambar yabo a cikin kasar.