Ministan babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja Nyesome Wike ya gabatar da sabuwar dokar filaye da za ta fara aiki daga ranar 21 ga Afrilu, 2025.
Dokar da ta haifar da muhawara mai zafi tsakanin masu ruwa da tsaki, inda ake ba da shawarwari kan matakan da mazauna Abuja za su dauka don kare kadarorinsu.
A cikin sanarwar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, an bayyana cewa dokar za ta taimaka wajen samun kudaden shiga ga hikumar babban birnin tarayya FCDA. Sai dai, wasu ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa kan yadda dokar za ta shafi masu mallakar filaye a Abuja.