Gwamna Umo Eno na Jihar Akwa Ibom ya ce jam’iyyarsa ta PDP da jam’iyyar APC na da akidar siyasa iri daya.
Hakan na zuwa ne a yayin da ake ta rade-radin cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya.
Gwamna Eno,ya kalubalanci kowa da kowa da ya tabbatar masa da akasin haka cewa jam’iyyun biyu ba su kamanceceniya da juna a siyasance.