Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa akwai yiyuwar jam’iyyar APC mai mulki za ta rabu nan ba da jimawa ba, tare da yiwuwar shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, da wasu shugabanni su sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Sule Lamido, wanda shi ne tsohon ministan harkokin waje na Nijeriya kuma jigo a jam’iyyar PDP, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin musamman a taron gangamin jam’iyyar PDP da aka gudanar a dandalin Aminu Kano da ke jihar Jigawa.
Jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa shugabanni da dama na jam’iyyar PDP ciki ha da sanatoci, gwamnoni, ‘yan majalisar wakilai da sauransu sun sauya sheka zuwa APC a shirye-shiryen zaben 2027.
Sai dai a martaninsa, daraktan yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Bala Ibrahim, ya shaida wa Daily Trust cewa mafarki ne kawai jam’iyyar PDP ke yi.