Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bayyana cewa babu wata gwamnati a tarihin Nijeriya da ta zuba jari a harkar noma kamar yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi cikin shekaru biyu da suka gabata.
Gwamna Uba Sani ya ce matakan da Tinubu ya dauka sun taimaka matuka wajen rage talauci a Arewacin kasar.
Uba Sani ya jaddada irin goyon bayan da ake bai wa kananan manoma, tallafin takin zamani, da kuma taimakon kudi ba tare da la’akari da jam’iyya ba ga jihohi.
Ya danganta wadannan kokari da cike gibin ababen more rayuwa, samar da ayyukan yi, da kuma rage talauci a cikin al’umma.